logo

HAUSA

Sin: Ba bukatar Amurka ta damu da halin da Hong Kong ke ciki

2022-05-16 20:44:43 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce kamata ya yi Amurka ta maida hankali kan matsalolin dake gaban ta, maimakon nuna damuwa da yanayin da yankin Hong Kong ke ciki.

Kalaman na Zhao na zuwa ne, bayan da a baya bayan nan kakakin majalissar wakilan Amurka Nancy Pelosi, ta furta wasu maganganu marasa tushe game da yankin na Hong Kong.

Da yake tsokaci kan kalaman nata, yayin taron manema labarai na Litinin din nan, Zhao Lijian ya jaddada cewa, tun bayan fara aiwatar da dokar tsaron kasa a Hong Kong, yanayin yankin ya kyautata matuka, ta yadda burin ‘yan siyasar Amurka game da HK din ya zama mafarki. Ya ce a yanzu haka, Amurka na fama da hauhawar farashin kayayyaki, yayin da annobar COVID-19 ta hallaka al’ummar kasar sama da miliyan 1, baya ga laifuka masu nasaba da hare-haren bindiga dake kara aukuwa akai akai a kasar.

Don haka dai Zhao Lijian ke cewa, idan Nancy Pelosi na da lokaci da kuzarin aiki, kamata ya yi ta maida hankali ga magance kalubalolin kasar ta, maimakon damuwa da halin da yankin HK ke ciki.    (Saminu)