logo

HAUSA

Tsohon CEO na Goldman Sachs: Amurka na fuskantar babbar barazanar fadawa matsalar tattalin arziki

2022-05-16 10:51:28 CMG Hausa

Lloyd Blankfein, tsohon CEO na bankin Goldman Sachs, daya daga cikin bankunan zuba jari mafi girma a duniya, ya ce akwai bukatar Amurka ta zauna cikin shirin tunkarar matsalar tattalin arziki.

Yayin wata hirar da kafafen yada labarai a jiya, Lloyd Blankfein ya ce, ya yi ammana cewa Amurka na fuskantar babbar barazanar fadawa matsalar tattalin arziki. Duk da cewa babban bankin kasar na da dabaru masu karfi na tunkarar matsalar, zai yi wuya a ga tasirinsu wajen sauya yanayin tattalin arzikin. Ya kara da cewa, kamar tafiyar da katafaren kamfani, akwai bukatar Amurka ta shiryawa tunkarar wadannan barazana. (Fa’iza Mustapha)