logo

HAUSA

IMF ta daga matsayin RMB da dala a tsarin musayar kudi na SDR

2022-05-16 10:50:30 CMG Hausa

Asusun ba da lamuni na duniya wato IMF, ya sanar da karin darajar kudin kasar Sin na RMB da dalar Amurka, a cikin tsarin musayar kudaden ketare (SDR), bayan kammala nazari na tsawon shekaru.

Wannan shi ne nazari na farko da aka yiwa tsarin na SDR , tun lokacin da RMB ya zama kudi na biyar a hukumance a cikin tsarin musayar kudaden na SDR a cikin shekarar 2016. Sake bitar tsarin na zuwa ne, bayan shekara daya da yadda aka tsara tun farko, saboda cutar COVID-19.

Sake fasalin tsarin, yana nuna ’yar karuwar ma'aunin darajar dalar Amurka da RMB da ’yar karamar karuwa kan kudin euro, da Yen na Jafan da fam na Burtaniya.

Asusun na IMF dai, ya daga darajar dalar Amurka daga kashi 41.73 zuwa kashi 43.38 cikin 100, yayin da darajar RMB na kasar Sin ta karu daga kashi 10.92 zuwa kashi 12.28 cikin 100. (Ibrahim)