logo

HAUSA

Putin: Neman zama mamban NATO babban kuskure ne

2022-05-15 17:18:19 CMG Hausa

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da takwaransa na kasar Finland, Sauli Niinisto, sun tattauna ta wayar tarho a jiya Asabar, inda suka tabo batun aniyar Helsinki na neman shiga kungiyar tsaron hadin gwiwa ta NATO.

A yayin tattaunawar wadda kasar Finland ta shirya, shugaban Niinisto ya sanar da Putin aniyar kasar Finland na neman zama mamba a kungiyar tsaron NATO nan da wasu kwanaki masu zuwa, kamar yadda sanarwar da ofishin shugaban kasar Finland din ta fitar.

Sannan kuma, fadar Kremlin ta fidda sanarwar dake bayyana cewa, Putin ya jaddada cewa, yin watsi da asalin manufar zama kasar ‘yan ba ruwanmu babban kuskure ne, kasancewar babu barazanar tsaro da kasar Finland ta ke fuskanta.

Sanarwar ta ce, Putin ya bayyana damuwa cewa, yunkurin Helsinki na neman shiga kungiyar tsaron NATO,  na iya haifar da mummunan tasiri na gurgunta dangantakar dake tsakanin kasashen Rasha da Finland.

Yayin tattaunawa kan batun halin da ake ciki a Ukraine kuwa, Putin ya ce, tattaunawar zaman lafiyar da aka shirya tsakanin wakilan Rasha da na  Ukraine, “Kiev ce ta dakatar da ita, kasancewar bata dauki batun tattaunawar da muhimmanci ba”.(Ahmad)