logo

HAUSA

Xi Jinping ya isar da sakon jaje ga sabon shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa bisa rasuwar shugaba Sheikh Khalifa

2022-05-15 20:50:55 CMG Hausa

Jiya Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika sakon ta’aziyya ga sabon shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, bisa rasuwar shugaban kasar, Sheikh Khalifa.

A madadin gwamnati gami da daukacin al’ummar kasar Sin, shugaba Xi ya bayyana matukar alhinin rasuwar Sheikh Khalifa, tare kuma da jajantawa iyalan marigayin da al’ummar Hadaddiyar Daular Larabawa baki daya. (Murtala Zhang)