logo

HAUSA

Yau ake cika shekaru hudu da kafa kwamitin kula da harkokin waje na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin

2022-05-15 17:11:12 CMG Hausa

An kira taro na farko na kwamitin kula da harkokin waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a ranar 15 ga watan Mayun shekara ta 2018, al’amarin da ya shaida cewa an kafa kwamitin a hukumance, kuma an kafa alkibla ga ayyukan diflomasiyyar kasar Sin a sabon zamanin da muke ciki.

Game da ci gaban harkokin diflomasiyyar kasar Sin a shekarun da suka gabata, shehun malami Wang Yiwei, daga tsangayar koyon ilimin diflomasiyya ta cibiyar nazarin dangantakar kasa da kasa ta jami’ar Renmin ta kasar Sin, ya bayyana cewa, duniya ta shiga cikin wani sabon lokaci da ake fuskantar sabbin sauye-sauye, ganin yadda zamaninmu ke canjawa gami da yadda cutar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa. Kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen aiwatar da manufar dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya, don kara bude kofa ga kasashen waje, da nuna hakuri da samar da ci gaba da daidaito ga kowa da kowa.

A watan Satumbar bara, a wajen babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira a maida hankali kan bukatun kasashe masu tasowa a fannin samar da ci gaba. Daga bisani, shugaba Xi ya kuma yi kira a fannin tabbatar da tsaron duniya a wajen taron shekara-shekara na 2022 na dandalin Boao na Asiya, a wani kokari na fitar da duniya daga cikin mawuyacin halin tsaron da take ciki. Wang Yiwei ya kara da cewa, duk kiran da shugaba Xi ya yi ya shaida hikimomin kasar Sin, inda ya ce:

“Kasar Sin ta yi kira a samar da ci gaba ga duk duniya, da maida hankali kan muradun samar da ci gaba mai dorewa na MDD, saboda ci gaba shi ne jigon warware dukkan matsalolin dan Adam. Amma, ba za’a iya raba ci gaba da tsaro ba, don haka shugaba Xi ya kara yin kira a fannin tsaron duniya a wajen dandalin Boao na nahiyar Asiya da aka yi a bana. Ya dace a hada batun tabbatar da tsaro tare da samar da ci gaba a lokaci guda, al’amarin da zai zama wani muhimmin dandalin hadin-gwiwa don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, a yayin da ake kokarin raya shawarar ‘ziri daya da hanya daya’.” (Murtala Zhang)