logo

HAUSA

Masana sun yi Allah wadai da yunkurin Amurka na neman dakile cigaban al’ummar Xinjiang

2022-05-15 16:38:49 CMG Hausa

Kwararrun masanan kasar Sin sun soki lamirin ‘yan siyasar kasar Amurka masu adawa da kasar Sin, wadanda ke shirya makarkashiya domin hana al’ummar yankin Xinjiang damamamkinsu na cigaba ta hanyar yada karairayin cewa, wai ana tilasta aikin kwadago a shiyyar.

Sun yi Allah wadan ne a yayin taron manema labarai da aka gudanar a ranar Juma’ar da ta gabata a Urumqi, babban birnin jahar Xinjiang mai zaman kanta ta Uygur ta kasar Sin.

Cao Wei, wani shehun malamin jami’ar Lanzhou, ya bayyana cewa, sakamakon fargabar kakaba takunkumi daga kasar Amurka, ya sa wasu daga cikin kamfanoni ba su son daukar ma’aikatan kwadago ‘yan kabilan Uygur, inda hakan ke haifar da karuwar rashin ayyuka yi da kuma haifar da koma bayan cigaban yanayin zaman rayuwar al’ummar Uygur.

Shi ma Ildos Murat, mataimakin shugaban tarayyar kungiyoyin ‘yan kasuwan yankin Xinjiang, ya bayyana cewa, gaskiyar magana shi ne, Amurka ita ne kasar da har yanzu ayyukan kwadago na tilas ke cigaba da wanzuwa har a wannan karni na 21, yayin da ‘yan cin rani su ne matsalar tafi shafa, kuma gwamnatin Amurka ta kawar da kanta daga sauke nauyin dake wuyanta wajen ba su kariya.(Ahmad)