logo

HAUSA

Yankin yammacin Afrika na gab da fara samar da alluran rigakafin cututtuka

2022-05-14 16:11:57 CMG HAUSA

 

Darakta janar na hukumar lafiya ta yammacin Afrika WAHO Stanley Okolo, ya ce yankin na gab da fara samar da alluran rigakafin cututtuka daban-daban.

Stanley Okolo, ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai da aka yi jiya, bayan kammala taro karo na 23 na ministocin lafiya na kasashe mambobin kungiyar ECOWAS.

A cewarsa, yankin zai fara samar da rigakafin cututtuka daban-daban, ciki har da na COVID-19 da Shawara da cutar cizon kare da na maciji, da nufin zama mai dogaro da kansa wajen samar da rigakafi da kuma wadatarsu.

Ya kara da cewa, sun samu kamfanoni 5 da nazari ya nuna cewa, suna gab da samar da rigakafin a yankin yanzu. 2 daga cikinsu kamfanoni ne na kasar Ghana, 2 kuma na Nijeriya sai kuma 1 daga kasar Senegal.

Ya ce, daga matsakaici zuwa dogon zango, yankin zai iya samar da nau’ikan alluran riga kafi 22 da zarar an karfafa masana’antarsa na harhada magunguna.

Bugu da kari, ya ce hukumar lafiyar ta yammcin Afrika WAHO, ta hada hannu da hukumar raya masana’antu ta MDD, domin samar da dabarun tabbatar da kamfanonin harhada magungunan na aiki yadda ya dace, a matsayin wani kokari na tabbatar da cewa, kayayyakin da za su samar sun kai matakin inganci da ake bukata. (Fa’iza Mustapha)