logo

HAUSA

Ya kamata Sin da Amurka su kara hadin gwiwa a fannin aikin noma

2022-05-14 16:48:41 CMG Hausa

An gudanar da taron tattauna bunkasa aikin noma da yankunan karkara tsakanin kasashen Sin da Amurka ta yanar gizo a baya bayan nan, wanda kwalejin ilmin bunkasa kasa da kasa da aikin noma ta duniya, ta jami’ar ilmin aikin noma ta kasar Sin ta dauki bakuncinsa. Mahalartar taron na ganin cewa, ya kamata Sin da Amurka su kara hadin gwiwa a fannin aikin noma, suna cewa, hakan zai amfanawa kasashen biyu, har ma da samar da gudummawa ga tabbatar da wadatar hatsi a duniya.

Bisa kididdigar da aka yi, yawan kudin cinikin aikin noma da aka samu tsakanin Sin da Amurka a shekarar 2021 ya kai dalar Amurka biliyan 46.4, wanda ya kai matsayin koli a tarihi. Tsohuwar gwamnar jihar Iowa ta kasar Amurka, Patty Judge ta bayyana cewa, kara hadin gwiwar cinikayyar aikin noma tsakanin Amurka da Sin yana da muhimmanci sosai kan aikin noma, kana kasashen biyu za su samu moriyar juna. Ta ce a halin yanzu, ya kamata kasashen biyu su nemi hanyoyi da damar yin mu’amala da juna, kana mu’amalar dake tsakanin kwararru na kasashen 2 masu nazarin aikin noma, za ta taimakawa raya dangantakar dake tsakaninsu.

Shugaban kwalejin nazarin tattalin arziki da manufofi a fannin abinci na duniya ta jami’ar ilmin aikin noma ta kasar Sin, Fan Shenggen ya bayyana a gun taron cewa, farashin abinci a duniya yana karuwa, yana mai cewa hakan ya kawo barazanar matsalar yunwa ga jama’ar Afirka da kudancin Asiya. Ya ce kiyaye farashin abinci a duniya muhimmin nauyi ne da ya kamata Sin da Amurka su sauke don samarwa kowa abinci mai inganci kuma mai gina jiki, kana aiki ne da ya shafi kowane bangare, don haka ya kamata dukkan kasashen duniya su yi kokarin hada hannu wajen daidaita matsalar. (Zainab)