logo

HAUSA

Xi da takwaransa na Croatia sun taya juna murnar cika shekaru 30 da kulla huldar jakadanci

2022-05-13 19:36:11 CMG HAUSA

 

            

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Croatia Zoran Milanovic, suka yi musayar sakon taya juna murnar cika shekaru 30 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi ya ce, saboda kokarin hadin gwiwa da bangarorin biyu suka yi, ya sa kasashen Sin da Croatia sun samu amincewar juna a fannin siyasa, kana sun samu sakamako mai kyau bisa hadin gwiwarsu wajen aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, lamarin da ya samar da moriya ga jama'ar kasashen biyu.

Xi ya kara da cewa, yayin da ake fuskantar kalubalen da annobar COVID-19 ta haifar, kasashen Sin da Croatia sun hada kai wajen yakar annobar tare da bude wani sabon babi na sada zumunta tsakanin kasashen biyu.(Ibrahim)