logo

HAUSA

Jakadan Sin: Wanzuwar zaman lafiya ne kariya mafi kyau ga yara a Ukraine

2022-05-13 11:27:41 CMG Hausa

Wakilin kasar Sin ya bayyana a ranar Alhamis cewa, cimma nasarar wanzuwar zaman lafiya shi ne kariya mafi kyau ga kananan yara a Ukraine.

Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya bayyana cewa, neman yadda za a cimma zaman lafiya shi ne kariya mafi kyau ga yara. Tattaunawar sulhu da neman cimma matsaya su ne hanyoyi mafiya tabbaci kuma hanyoyi masu billewa da za su kai ga tsagaita bude wuta. Ya kamata al’ummun kasa da kasa su karfafa gwiwa ga Rasha da Ukraine don su amince ga komawa kan teburin tattaunawar sulhu, kuma a ci gaba da bin matakan siyasa domin mayar da zaman lafiyar, in ji wakilin na Sin.

Jakadan na Sin ya ce, sanya takunkumi ba zai kawo zaman lafiya ba, sai dai ma ya kara ta’azzarar rikicin da ake fama da shi, da haddasa tsananin karancin abinci, da makamashi, da haifar da karayar tattalin arzikin duniya baki daya, kana lamarin zai iya yin sanadiyyar jefa kananan yara a fadin duniya cikin tsananin wahala. Yaran dake rayuwa a kasashen da ake fama da yake-yake, kamar Afghanistan, da Yemen, da kusurwar Afrika, da ma yankin Sahel, suna dandana kudarsu sakamakon karancin tallafin jin kan bil adama.

Mr. Dai ya ce, kasar Sin tana kara yin kira ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki da su shiga taitayinsu, kana su kai zuciya nesa, su guji haddasa kiyayya da kawo baraka, kana su tsaya tsayin daka wajen kokarin kashe wutar rikicin Ukraine a kan lokaci, domin a samarwa yara kyakkyawar makoma mai cike da zaman lafiya da lumana. (Ahmad)