logo

HAUSA

Biden ya ce yadda COVID-19 ta kashe Amurkawa miliyan 1 mummunan bala’i ne a tarihin kasar

2022-05-13 11:25:49 CMG Hausa

Yayin karrama Amurkawa miliyan 1 da cutar COVID-19 ta hallaka, adadi mafi yawa a duniya, shugaban kasar Amurkar Joe Biden, ya bayyana adadin da cewa mummunan bala’i a tarihin kasar.

A sanarwar da fadar White House ta fitar, Biden ya ce, “kowane rai hasara ce da ba za a iya maye gurbinta ba.

Ya ce kowane rai yana da nasaba da wani iyali, ko unguwa, ko kuma kasa wanda har aka sauya shi saboda wannan annobar, Biden ya bukaci Amurkawa da kada su firgita sakamakon wannan tashin hankali, sai dai ya umarce su da su tsaya tsayin daka don yakar wannan annobar.

Alkaluman baya bayan nan da jami’ar Johns Hopkins ta fitar ya nuna cewa, jimillar adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a Amurka ya kai miliyan 82, kuma shi ne adadi mafi yawa a duniya. (Ahmad)