logo

HAUSA

An gudanar da taron karawa juna sani game da kare hakkin bil adama na Sin da EU

2022-05-13 16:22:44 CMG Hausa

A ranar 10 ga watan nan na Mayu ne aka gudanar da taron karawa juna sani na bana, don gane da batun kare hakkin bil adama na Sin da kungiyar tarayyar Turai EU.

Cibiyar bincike game da kare hakkin bil adama ta Sin, da kungiyar kawancen Sin da Austria ne suka shirya taron cikin nasara. An kuma gudanar da shi a birnin Wuhan na kasar Sin, da kuma birnin Vienna na Austria a fili da kuma ta yanar gizo.

Taron na shekarar 2022, ya hallara wakilai daga ofishin hukumar kare hakkin bil adama ta MDD, da kwararru sama da 100, da masana a fannin kare hakkin bil adama na Sin, da Austria, da Birtaniya, da Jamus, da Hungary, da Italiya, da Girka, da Sifaniya, da karin wasu kasashen, inda aka tattauna batutuwa masu alaka da kimiyya da fasaha da kare hakkin bil adama. (Saminu)