logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga bangarori daban-daban da su goyi bayan tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine

2022-05-13 10:46:37 CMG HAUSA

 

Jiya Alhamis, kwamitin kula da hakkin dan Adam na MDD, ya kira wani taro na musamman kan batun Ukraine. Zaunannen, wakilin Sin dake sashen Geneva na MDD Chen Xu, ya ba da jawabi a yayin taron, inda ya kalubalanci bangarorin da abin ya shafa, da su goyi bayan yin shawarwari tsakanin Rasha da Ukraine bisa ra’ayin hadin kai, da samun zaman lafiya mai dorewa, ta yadda za a kafa tsarin tsaron duniya, da shiyya-shiyya mai daidaito da amfani a dogon lokaci. Chen Xu ya ce:

“Sin na goyon bayan duk wani matakin dake iya sassauta matsalar jin kai da Ukraine ke ciki. Tana kuma yin kira ga bangarori daban-daban da abin ya shafa, da su mutunta dokar jin kai ta kasa da kasa, da daukar matakan da suka dace don kiyaye lafiyar fararen hula, da kiyaye moriya mai tushe, da bukatar jin kai na mata, da kananan yara da sauransu. 

“Sin ta gabatar da shawarwarinta guda shida, game da halin jin kai da Ukraine ke ciki, inda kuma tuni ta baiwa kasar tallafin jin kai. Sin ta ce kamata ya yi bangarori daban-daban su goyi bayan shawarwari tsakanin kasashen biyu, don tabbatar da zaman lafiya, ta yadda za a kiyaye hakkin bil Adama na fararen hular Ukraine. Hakan kuma, kamata ya yi kasashen duniya su kafa yanayi mai kyau ga shawarwarin kaucewa kawo cikas gare su. Sin ta yi imanin cewa, ba wata kasa dake iya samun cikakken tsaro, ta hanyar ganin saura na cikin rigingimu, don haka dole ne a yi hadin kai don kafa wani tsarin tsaro mai dorewa a duniya, da ma shiyya-shiyya.” (Amina Xu)