logo

HAUSA

Sin ta mai da martani game da gyaran “jerin batutuwan da ke shafar huldar da ke tsakanin Amurka da Taiwan” da Amurka ta yi

2022-05-12 13:17:30 CMG Hausa

Tashar yanar gizo ta ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka, ta sabunta “jerin batutuwan da ke shafar huldar da ke tsakanin Amurka da Taiwan” da ta gyara. A yayin da yake amsa tambayar dan jarida game da batun, a gun taron manema labarai da ya gudana a shekaran jiya da yamma, kakakin ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin Zhao Lijian ya ce, Sin daya tak ce a duniya, kuma Taiwan wani bangare ne da ba za a iya raba shi daga kasar ba, kuma gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin ita ce kadai halastaciyyar gwamnati da ke iya wakiltar kasar. Wannan ka’ida ce da daukacin kasashen duniya suka amince da ita.

Zhao ya jaddada cewa, ba za a iya gyara tarihi ba, kuma ba za a iya yin watsi da gaskiya ba. Amurka ta taba yin alkawarin amincewa da kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, cikin sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da ta fitar tare da kasar Sin.

Munafunci dai dodo ne da kan ci mai shi, yadda kasar Amurka ta gyara jerin batutuwan da ke shafar huldar da ke tsakaninta da yankin Taiwan, a yunkurin sauya yanayin da ake ciki a yankin.  (Lubabatu)