logo

HAUSA

An samu dan hauhawar farashin kayayyakin masarufi a kasar Sin a watan Afrilu

2022-05-12 11:31:52 CMG Hausa

Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta samar a jiya sun yi nuni da cewa, illolin da annobar Covid-19, da ma hauhawar farashin kayayyaki a fadin duniya suka haifar, sun sa farashin kayayyakin masarufi yana dan hauhawa kadan a kasar Sin, sakamakon matakan da aka dauka na kiyaye farashinsu.

Alkaluman sun yi nuni da cewa, ma’aunin farashin kayayyakin masarufi, wato CPI, ya karu da kaso 0.4%, idan an kwatanta da na watan da ya gabata, da ma kaso 2.1% idan an kwatanta da na bara.

Farashin abinci ya karu da kaso 0.9%, wanda a watan da ya gabata ne ya ragu da kashi 1.2%, a yayin da farashin kayayyakin da ba na abinci ba ya karu da kashi 0.2%.

A game da wannan, manazarciya a cibiyar nazarin harkokin tattalin arziki daga manyan fannoni ta kasar Sin, Madam Guo Liyan ta yi nuni da cewa,“Dalilin da ya sa muka kai ga kayyade hauhawar farashin kayayyakin masarufi da kimanin 2%, shi ne kwararan matakan da aka dauka na kiyaye farashin kayayyakin masarufi, da ma kara karfin samar da kayayyaki, matakan da suka aza harsashin kiyaye farashin kayayyaki a shekarar da muke ciki.” (Lubabatu)