logo

HAUSA

Kasar Amurkan ta samar da kayan yaki na zamani ga Ukraine a karon farko tun farkon fara yaki

2022-05-12 12:31:03 CMG HAUSA

 

A sanarwar da shafin intanet na "Defense News" na kasar Amurka ya wallafa, an bayyana cewa, sashen kula da tsaron Amurka a kwanan nan ya aike da rukunin makaman yaki da wasu kayayyakin aiki da kudinsu ya kai dala miliyan 150 ga kasar Ukraine. Kayayyakin da Amurkar ta aike da su a wannan karo, sun hada da na'urori masu aikin lantarki kuma masu lalata makamai. Shi ne karon farko da Amurka ta samar da makaman yaki na zamani ga Ukraine tun bayan da kasar Rasha ta kaddamar da ayyukan soji na musamman a Ukraine, a cewar babban jami’in tsaron Amurka.

Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Amurka ta samar da na’urorin zamani dake lalata makaman yaki domin baiwa Ukraine karin damar kaddamar hare-haren yadda ya kamata a wasu kebabbun yankuna. Rahoton ya bayyana cewa, Amurka ta fara shirin samarwa Ukraine muhimman na’urorin gidajen radiyo na zamani tun shekaru da dama da suka gabata, domin kare fannin sadarwa da kuma yakar masu yin kutse ga kasar. (Ahmad)