logo

HAUSA

Kasashen BRICS Za Su Bullo Da Tsarin Gargadin Barkewar Annoba

2022-05-11 19:25:02 CMG HAUSA

A jiya ne, taron ministocin kiwon lafiya na kasashe mambobin BRICS karo na 12, ya amince cewa, kasashen BRICS wato Brazil, Rasha, Indiya, China da South Africa za su kaddamar da tsarin gargadi na tunkarar cututtuka masu yawa.

Kasar Sin, wadda ke zama shugabar karba-karba ta kungiyar BRICS ta wannan shekara ce ta dauki nauyin taron, wanda ya gudana ta kafar bidiyo. Sama da mahalarta 70 ne suka halarci taron da suka hada da ministocin lafiya daga kasashen BRICS, da mataimakin babban darektan hukumar lafiya ta duniya.

A yayin taron, wakilai sun yi tattaunawa mai zurfi, kan batutuwa daban-daban, kamar rigakafin cutar COVID-19, da gina sabon tsarin kiwon lafiya da harkar kula da lafiya na zamani.

Shugaban hukumar kula da lafiya ta kasar Sin Ma Xiaowei, ya gabatar da manufofin kasar Sin game da yaki da cutar COVID-19, da suka hada da gano da kuma dakile cutar nan da nan. Ya kuma yi karin haske kan matakan kasar Sin na kiyaye daidaito tsakanin rigakafin cututtuka da ci gaban tattalin arziki.

Ma Xiaowei ya bayyana cewa, kasar Sin ta ba da gagarumar gudummawa a kokarin yaki da cutar a duniya, ta hanyar samar da kayayyakin kiwon lafiya, da tura ma'aikatan lafiya. Ya kara da cewa, ya zuwa yanzu, kasar Sin ta samar da alluran rigakafin COVID-19 sama da biliyan 2.2 ga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 120. (Ibrahim)