logo

HAUSA

Ana fatan Amurka za ta kare ‘yan kasar miliyan 100 daga kamauwa da cutar COVID-19

2022-05-11 19:35:54 CMG Hausa

Wani babban jami’in gwamnatin kasar Amurka ya bayyana a kwanakin baya cewa, kasar Amurka za ta fuskanci kalubalen yaduwar cutar COVID-19 mai tsanani a lokacin kaka da sanyi na shekarar bana, kuma mai yiwuwa ne ‘yan kasar miliyan 100 za su kamu da cutar COVID-19. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau cewa, Sin ta damu da yadda jama’ar kasar Amurka suke fuskantar yanayin yaduwar cutar COVID-19 a kasar. Sin tana fatan kasar Amurka za ta yi kokarin daukar matakan yaki da cutar, kuma ba za ta bari hasashen maras dadi da jami’in gwamnatin kasar ya yi, ya zama gaskiya ba. (Zainab)