logo

HAUSA

Sin tana shirin hana yaduwar cutar COVID-19 cikin hanzari

2022-05-11 20:42:35 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya jaddada a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, manufar kandagarkin cutar COVID-19 da Sin ta gudanar ba ta nufin babu wanda ya kamu da cutar a kasar, manufar ita ce gano da kuma hana yaduwar cutar cikin hanzari, da tabbatar da lafiyar jama’ar kasar Sin fiye da biliyan 1 da miliyan 400, da kuma farfado da tsarin zamantakewar al’ummar kasar yadda ya kamata. (Zainab)