logo

HAUSA

Gidauniyar Tallafawa Demokiradiya Ko Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasashe?

2022-05-11 15:54:34 CMG Hausa

A duk lokacin da aka ambaci asusu ko gidauniya, abin da zai fadowa mutum shi ne, aikin taimako ko inganta rayuwar al’umma a fannoni daban-daban, kamar lafiya, Ilimi, muhalli, mata har ma a wasu lokuta da kananan yara da sauransu.

Sai dai sabanin irin asusu ko gidauniyar da al’umma suka sani, har ma suka ci moriyarsu, gidauniyar NED ta Amurka, wata gidauniya ce da Amurkar ta kirkiro da nufin tayar da hargitsi da neman tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe da sunan raya demokiradiya.

A kwanakin nan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wasu jerin shaidu game da asusun demokiradiya na kasar Amurka NED. Wadannan shaidu masu kunshe da manyan sassa shida da kalmomi kimanin 12,000, sun bankado hakikanin tsarin asusun, ta hanyar misalai guda 100 da aka tattara daga rahotanni.

Bayanai na nuna cewa, kasar Amurka ta dade tana amfani da karfin tuwo wajen baiwa demokuradiyya makamai, da yaki da demokradiyya da sunan shimfida demokuradiyya, da haddasa rarrabuwar kawuna, da yin katsalandan a harkokin cikin gidan wasu kasashe, lamarin da ya haifar da mummunar illa.

A matsayinsa na mai nuna fin karfi da aikata ashsha da sunan bayar da taimako na gwamnatin Amurka, asusun NED ya keta halascin gwamnatocin wasu kasashe tare da bunkasa makiya masu goyon bayan Amurka ta hanyar fakewa da sunan “inganta tsarin demokuradiyya”.

Asusun NED ya kuma fadada aikin makircinsa zuwa kasar Sin, tare da zuba kudade masu tarin yawa a duk shekara, don tunzura neman "'yancin kai a Xinjiang, da Hong Kong da Tibet" don aiwatar da ayyukan kin jinin Sinawa. Haka kuma asusun ya hada kai da masu neman ‘yancin Taiwan a wani yunkuri na haifar da rarrabuwar kawuna da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar mashigin tekun Taiwan, lamarin da ya haifar da fushi da adawa daga al'ummomi dake bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan.

Ko ma dai mene ne, yanzu dai asirin wannan asusu ya tonu, kuma duk wani makirci da neman tayar da zaune tsaye ko raba kan al’ummun kasashe ta hanyar fakewa da gidauniya ko asusun raya tsarin demokiradaya da ‘yanci ba zai taba yin nasara ba.(Ibrahim Yaya)