logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Samar Da Sama Da Alluran Rigakafin Cutar COVID-19 Biliyan 2.2 Ga Duniya

2022-05-11 20:13:42 CMG HAUSA

Kasar Sin ta samar da sama da alluran rigakafin cutar COVID-19 biliyan 2.2 ga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 120, galibinsu kasashe masu tasowa.

Kasar Sin ita ce kasa ta farko, da ta goyi bayan hana ‘yancin mallakar fasaha game da allurar rigakafin COVID-19 da gudanar da hadin gwiwar samar da alluran tare da sauran kasashe masu tasowa. Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta aiwatar da hadin gwiwar samar da allurar rigakafi tare da kasashe 13, tare da sanya hannu kan takardun hadin gwiwa da kasashe guda takwas.

Tun bayan barkewar cutar COVID-19, kasar Sin ta gudanar da ayyukan jin kai na gaggawa a duniya mafi girma da ba a taba ganin irinsu ba a tarihin jamhuriyar jama'ar kasar Sin.

Bayanan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayar Larabar nan na nuna cewa, ya zuwa farkon watan Mayu, gaba daya kasar Sin ta ba da kayayyakin yaki da cutar COVID-19 ga kasashe 153 da kuma kungiyoyin kasa da kasa 15, ciki har da rigunan kariya biliyan 4.6 da abin rufe baki da hanci sama da biliyan 430.

Bugu da kari, kasar Sin ta aike da tawagogin kwararrun ma’aikatan lafiya 37 zuwa kasashe 34, tare da yin musayar kwarewa da kandagarkin annobar COVID-19 da sama da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 180.(Ibrahim)