logo

HAUSA

Sin ta bada gudunmawar riga-kafin Sinovac da kayayyakin lafiya ga Benin

2022-05-11 10:57:09 CMG Hausa

A jiya Talata jamhuriyar Benin ta karbi rukunin alluran riga-kafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinovac, da kayayyakin kiwon lafiya wadanda gwamnatin kasar Sin ta bayar a matsayin gudunmawa.

Babban jami’in ofishin jakadancin Sin dake kasar Benin, Yan Yan, ya jagoranci bikin mika tallafin da yammacin ranar Talata, tare da babban darakta a ma’aikatar lafiyar jamhuriyar Benin, Petas Akogbeto, wanda aka gudanar a Cotonou, birnin tashar ruwan jamhuriyar Benin.

Gudunmawar dai ta kunshi kwalaben alluran riga-kafi na kamfanin Sinovac, da sirinji, da na’urar daukar hoton jiki, da manyan na’urorin  binciken yanayin lafiyar jiki, da famfunan sirinji masu aiki da lantarki, da gadajen kwantar da majinyata, da sauran na’urorin ayyukan kiwon lafiya iri daban-daban.

Da yake jawabi a lokacin bikin mika kayayyakin, Yan ya ce, tallafin da kasar Sin ke baiwa Benin a fannin kiwon lafiya, alamu ne dake bayyana zurfin dangantakar dake tsakanin gwamnatocin kasashen biyu da kuma kyakkyawar abota a tsakanin al’ummun kasashen biyu.

Ya ce, “Sin da Benin abokai ne kuma ’yan uwan juna, wadanda ke da kyakkyawar hulda a fannin kiwon lafiya don yaki da annobar COVID-19.” (Ahmad)