logo

HAUSA

Sin ta bukaci hadin gwiwar kasa da kasa don tinkarar fari da kurkusowar Hamada

2022-05-10 11:13:47 CMG HAUSA

 

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yi kira a karfafa hadin gwiwar kasa da kasa domin tinkarar matsalolin fari da kurkusowar Hamada.

Wang, a matsayinsa na wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi wannan tsokaci ne a taron shugabanni da aka gudanar ta kafar bidiyo, game da warware matsalolin fari da daidaita yanayin gonaki.

Ya ce, “ya kamata mu sa kaimi wajen tinkarar batutuwan dake shafar fari wadanda ke damun kasashen Afrika, a ci gaba da inganta dokokin dake shafar yaki da matsalar fari, kana a gina wani tsari na adalci kuma muhimmin tsarin magance matsalolin kurkusowar Hamada.”

Wang ya jaddada cewa, kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa don gina muhalli mai launin kore karkashin “shawarar ziri daya da hanya daya”, da kuma hanyar wasu dabaru kamar dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika, da hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa. Kasar Sin za ta yi aiki tare da kasashen Afrika domin gina ni’imtacciyar Afrika mai launin kore.

Taron shugabannin game da batun tinkarar matsalar fari da daidaita yanayin gonaki, wani muhimmin taro ne da aka gudanar karo na 15 na babban taron masu ruwa da tsaki kan batun sauyin yanayi wato (COP15), karkashin yarjejeniyar shirin kawar da matsalar kurkusowar Hamada na MDD (UNCCD), wanda kasar Kwadebuwa ta karbi bakuncinsa. (Ahmad)