logo

HAUSA

Sin: Ko Wane Irin Tsarin Zabe Ake Aiwatarwa A Hong Kong Makiya Daga Waje Ba Su Da Ikon Tsoma Baki

2022-05-10 19:51:32 CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana cewa, wasu kasashen yammacin duniya da hukumomi, sun hada kai da juna, wajen yin katsalandan a zaben kantoman yankin musamman na Hong Kong, tare da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin.  Kuma kasar Sin tana adawa matuka tare da yin Allah wadai da wannan mataki.

Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, zaben kantoman yankin na Hong Kong karo na 6 da aka kammala, wata nasara ce da aka samu a sabon tsarin zabe na yankin Hong Kong. An gudanar da zabe bisa dokoki da ka’idojin da aka tsara, kuma cikin lumana da adalci. A hannu guda kuma sakamakon zaben kamar yadda aka yi tsammani, ya samu karbuwa daga wajen jama’a, abin da ke nuna hakikanin tsarin demokuradiyya.

Zhao ya jaddada cewa, Hong Kong wani yanki ne na kasar Sin. Duk wani irin tsarin zabe da yankin Hong Kong ya aiwatar, kuma ko wane tsarin raya demokuradiyya da Hong Kong ya yi amfani da shi, harkokin ne na cikin gidan kasar Sin kawai, kuma babu wasu makiya daga waje da ke da ‘yancin tsoma baki.(Ibrahim)