logo

HAUSA

An kira babban taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar CCYL

2022-05-10 10:51:02 CMG Hausa

Da safiyar yau Talata, an kira babban taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar kungiyar matasan kwaminis ta kasar Sin ko CCYL a takaice, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar,

Yayin taron, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasar, kana shugaban kwamitin aikin soja na kasar Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin jawabi.

Wakilai 13, wadanda matsakaicin shekarun haihuwarsu suka kai 28 kacal, sun halarci babban taron wakilan JKS na duk kasar a karon farko a watan Yulin shekarar 1921, inda suka sanar da kafuwar JKS, daga baya a karkashin jagorancin JKS, an kafa kungiyar matasan kwaminis ta kasar Sin a shekarar 1922.

Alkaluman takardar bayani mai taken “Matasan kasar Sin a sabon zamani” da aka fitar a kwanan baya, sun nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2021, gaba daya adadin ‘yan kungiyar matasan kwaminis ta kasar Sin ya kai miliyan 73.715. (Jamila)