logo

HAUSA

Kasar Sin ta soki Amurka kan jirkita bayanai game da yankin Taiwan

2022-05-10 19:27:28 CMG HAUSA

 

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Talatar nan, ta yi Allah wadai da yadda kasar Amurka take jirkita gaskiya game da batun da ya shafi yankin Taiwan, inda ta bukace ta da ta mutunta kudurin da ta dauka, na martaba manufar “kasar Sin daya tak a duniya”.

Rahotanni na cewa, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta goge kalaman da ke cewa "Taiwan wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba" da kuma cewa "Amurka ba ta goyon bayan 'yancin Taiwan" a wani muhimmin bayani da aka sabunta a shafinta na yanar gizo a ranar 5 ga watan Mayu.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shaidawa taron manema labarai da aka saba shiryawa a nan birnin Beijing cewa, manufar sabuwar dabarar ta bangaren Amurka, ita ce shafe manufar “kasar Sin daya tilo a duniya”.

Zhao ya ce, irin wadannan abubuwa na magudin siyasa da Amurka ke yi, da ke kokarin sauya matsayin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan, za su kona wadanda ke wasa da wuta.(Ibrahim)