logo

HAUSA

An harba kumbon dakon kaya na Tianzhou-4 cikin nasara

2022-05-10 10:14:54 CMG Hausa

Da sanyin asubar yau Talata 10 ga wata, an yi cikakkiyar nasarar harba kumbon dakon kaya na Tianzhou-4 da rokar Long March-7 Y5, daga filin harba kumbunan dake birnin Wenchang na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.

Mataimakin babban mai tsara fasalin kumbun dakon ‘yan sama jannati na kasar Sin Liu Jin ya yi tsokaci da cewa,

“Ina farin ciki kwarai yanzu, saboda rokar ta harba kumbon zuwa falakin da aka tsara, lamarin da ya shaida cewa, ma’aikatan nazarin fasahohin sararin samaniya sun samu sabon ci gaba, yadda ‘yan sama jannatin kasarmu za su gudanar da aikinsu bisa tushe mai inganci, ko shakka babu ci gaban da aka samu a bangaren yana da babbar ma’ana ga babban aikin nazarin sararin samaniyar kasar Sin, haka kuma zai taimakawa ci gaban wayewar kan bil adama.”

Makasudin harba kumbon dakon kaya na Tianzhou-4 yau shi ne samar da isassun kayayyaki ga ‘yan sama jannati guda uku, na kumbon dakon mutane na Shenzhou-14 da za a harba, zuwa tashar nazarin sararin samaniya ta kasar Sin a wata mai zuwa, inda za su sauka a ciki tare da gudanar da ayyuka na tsawon watanni shida. (Jamila)