logo

HAUSA

Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Faransa Ta Wayar Tarho

2022-05-10 21:07:48 CMG HAUSA

A yammacin yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron.

Yayin tattaunawar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a yayin da ake fuskantar manyan sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin shekaru 100, kasashen Sin da Faransa a matsayinsu na kasashe mambobin dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kana manyan kasashe masu cin gashin kansu, ya kamata su tsaya kan hakikanin manufar kulla huldar diflomasiyya mai 'yancin kai, da fahimtar juna, da hangen nesa, da samun moriyar juna da nasara tare, da tsayawa tsayin daka bisa manyan tsare-tsare da daidaita dangantaka, da mutunta muhimman moriya da manyan batutuwan dake shafar juna, da yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, da Sin da EU da matakan kasa da kasa.

Dangane da halin da ake ciki a kasar Ukraine, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin na inganta shawarwarin zaman lafiya ta hanyar da ta dace, kuma tana goyon bayan kasashen Turai da su dauki matakan tsaron kasashen Turai da kansu. Ya ce, wajibi ne mu yi taka tsantsan game da kafa wani rukuni na yin fito na fito, wanda zai haifar da babbar barazana ga harkar tsaro da zaman lafiyar duniya.

A nasa bangare kuwa, shugaba Macron ya bayyana cewa, game da batun Ukraine, bangaren Faransa na da ra'ayi kusan iri daya da bangaren Sin. Faransa da EU suna martaba dabarun 'yancin kai, kuma ba za su shiga cikin wani rukini na yin fito na fito ba. (Ibrahim)