logo

HAUSA

Kakakin ma’aikatar wajen Sin ya yi tsokaci kan hadarin fashewar iskar gas a otel din Cuba

2022-05-09 12:12:19 CMG Hausa

A ranar 6 ga wata, agogon kasar Cuba, hadarin fashewar iskar gas ya faru a wani otel dake Havana, fadar mulkin kasar Cuba, a sanadin haka an yi hasarar rayukan mutane da dukiyoyi masu yawa.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya yi tsokaci kan batun, inda ya ce sakamakon daddaden amincin gargajiya dake tsakanin kasashen Sin da Cuba, kasar Sin ta nuna ainihin juyayin rasuwar wadanda lamarin ya rutsa da su, tare kuma da jajantawa iyalansu, da fatan samun sauki ga wadanda suka ji rauni. A daidai wannan lokacin bakin ciki, gwamnatin kasar Sin da al’ummunta, suna goyon bayan gwamnati da al’ummun kasar ta Cuba.

Jiya Lahadi hukumar kiwon lafiyar jama’ar Cuba ta bayyana cewa, adadin mutanen da suka rasu yayin aukuwar hadarin ya karu zuwa 30. (Jamila)