logo

HAUSA

Sin: Dabarar makiya daga waje na kutsawa cikin Hong Kong ba zai yi nasara ba

2022-05-09 19:39:27 CMG HAUSA

 

Dangane da kalaman da kungiyar tarayyar Turai EU ta yi na neman bata sunan zaben kantoman yankin musamman na Hong Kong, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa Litinin din nan cewa, dabarar da EU da sauran makiya daga waje suka yi na tsoma baki a Hong Kong, ba zai taba yin tasiri ba.

Zhao Lijian ya bayyana imanin cewa, sabon kantoman zai jagoranci sabuwar gwamnatin yankin musamman na Hong Kong da jama'a daga sassa daban-daban, don samar da wani sabon yanayi na kyakkyawan shugabanci gami da jagoranci na gari a Hong Kong tare. Har ila yau, ya jaddada cewa, a daidai lokacin da sabon tsarin zabe na yankin na Hong Kong ya zauna da gindinsa ta kowane fanni, da kuma kyautata tsarin demokuradiyya, makiya daga waje kamar kungiyar tarayyar Turai sun kasa yin hakuri, inda suka yi nuni tare da yin katsalanda da neman bata sunan tsarin zaben da ma sakamakon zaben baki daya. Wannan ya fito da hakikanin manufarsu ta tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin da neman kawo cikas ga makoma da kwanciyar hankali a yankin Hong Kong ta hanyar fakewa da batun tsarin demokuradiyya da 'yanci.(Ibrahim)