logo

HAUSA

Za a harba kumbon dakon kaya na Tianzhou-4

2022-05-09 10:33:51 CMG Hausa

Kwanan baya, an riga an kammala jigilar kumbon dakon kaya na Tianzhou-4, da rokar Long March-7 Y5 zuwa filin harba kumbuna, inda za a harba shi cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Aikin da ake gudanarwa yana jawo hankalin bangarori daban daban, saboda harbar kumbon bangare a aikin gina tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin karo na farko, wanda za a yi a shekarar bana wato 2022.

Hakika an riga an harba kumbon dakon kaya irin na Tianzhou da rokar Long March-7 har sau uku, yanzu haka kuma za a harba nau’in kumbon a karo na hudu.

Shin ko aikin ya samu kyautatuwa idan aka kwatanta ayyukan da aka gudanar a baya? Babbar mai tsara fasalin rokar Long March-7 Shen Dan ta bayyana cewa, ma’aikatan kera rokar sun yi kokari matuka, domin kara kyautata ingancin rokar, ta hanyar harhada tsarin ba da jagorancin shawagi na BeiDou a cikin rokar, tare kuma da tantancewa bisa bukata. A cewarta:

“Mun kyautata ingancin rokarmu, kuma muna amfani da tsarin ba da hidimar shawagi na BeiDou, lamarin da ya nuna cewa, muna cike da imani kan ingancin tsarin matuka.” (Jamila)