logo

HAUSA

Kasuwancin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da 7.9% A Watanni Hudu Na Farko Na Bana

2022-05-09 19:32:23 CMG HAUSA

Alkaluman hukuma da aka fitar Litinin din nan sun nuna cewa, adadin kayayyakin da kasar Sin ta shigo da kuma fitar da su, ya karu da kashi 7.9 bisa dari zuwa yuan triliyan 12.58 a watanni hudun farko na shekarar 2022 bisa makamancin lokaci na bara.

A dalar Amurka kuwa, jimillar cinikin waje a tsawon lokacin, ta kai dalar Amurka tiriliyan 1.98, adadin da ya karu da kashi 10.1 bisa makamancin lokaci na bara, a cewar babbar hukumar kwastam ta kasar kasar Sin.

Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, yawan kayayyakin da Sin take fitarwa zuwa kasashen waje, ya karu da kashi 10.3 bisa dari zuwa yuan tiriliyan 6.97, yayin da kayayyakin da take shigowa da su daga kasashen waje suka karu da kashi 5 bisa dari zuwa yuan tiriliyan 5.61 a tsakanin watan Janairu zuwa Afrilu, lamarin da ya kai ga samun rarar ciniki da ya kai yuan tiriliyan 1.36.

Kasuwancin kasar Sin da manyan abokan cinikinta guda uku wato kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya, da kungiyar tarayyar Turai da Amurka, sun ci gaba da samun bunkasuwa.

Alkaluman babbar hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna cewa, a cikin wannan lokaci, karuwar darajar cinikin kasar Sin da wadannan abokan huldar kasuwanci guda uku, ta kai kashi 7.2 bisa dari, da kashi 6.8 cikin 100 da kuma kaso 8.7 bisa dari bi da bi.(Ibrahim)