logo

HAUSA

Putin ya aike da sakon murnar zagayowar ranar samun nasara kan mayakan Nazi ga shugabannin duniya

2022-05-09 13:30:39 CMG Hausa

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya aike da sakon taya murnar cika shekaru 77 da samun nasara kan mayakan Nazi ga shugabanni da jama’ar kasashen Azerbaijan da Armenia da Belarus da Kazakhstan da Kyrgystan da Moldova da Tajikistan da Turkmenistan da Uzbekistan.

Cikin sakon da ya aika a jiya, shugaban Rasha ya ce yana jinjina da girmama sojoji da sauran wadanda suka yi aiki a bakin daga ta hanyar sadaukarwa da nufin murkushe mayakan Nazi.

A cewar shafin intanet na fadar Kremlin, shugaban ya kuma aike da sakon gaisuwa ga mazan jiya na Ukraine wadanda suka fafata a yakin.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce a ranar Asabar kasar ta kammala bitar faratin soja na agayowar ranar nasarar yakin Nazi. Inda kusan mutane 11,000 da nau’ikan makamai da kayayyakin soji 131 da jiragen sama 77 suka shiga bitar.

Rasha kan gudanar da faretin soji a duk ranar 9 ga watan Mayun kowacce shekara domin tunawa da nasarar Tarayyar Soviet a yakinta da mayakan Nazi na Jamus.  (Fa’iza Mustapha)