logo

HAUSA

Serbia da Sin sun yi bikin tunawa da kisan ’yan jarida Sinawa yayin harin NATO yau shekaru 23 da suka wuce

2022-05-09 10:37:18 CMG Hausa

 

Al’ummu da wakilan gwamnatocin kasashen Serbia da Sin, sun gudanar da bikin tunawa da kisan wasu ’yan jarida Sinawa, yayin harin bam da kungiyar tsaro ta NATO ta kaddamar kan ofishin jakadancin Sin dake birnin Belgrade, lokacin da NATOn ke matsin lamba ga kasar Yugoslavia yau shekarar 23 da suka gabata.

A ranar Asabar din karshen mako, an kawata allunan dake jikin ginin tsohon ofishin jakadancin da furanni kala kala, wurin da a yanzu ya zama wata cibiyar al’adu ta zamani.

Da yake tsokaci kan haka, babban sakataren kungiyar ’yan jarida ta Serbia ko UNS Mr. Nino Brajovic, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, Serbia da Sin sun fara gudanar da bikin tunawa da wannan rana ne yau shekaru 10 da suka gabata.

Brajovic ya ce "A gani na, kungiyoyin ’yan jaridu na kasa da kasa ba su aiwatar da matakan hukunta kisan ’yan jaridun Sinawa yayin harin na NATO yadda ya kamata ba, kuma hakan kaucewa gaskiya ne. Muna matukar adawa da hakan gwargwadon ikon mu."

A ranar 7 ga watan Mayun shekarar 1999 ne, harin bam da ya fada kan ofishin jakadancin Sin dake Belgrade, ya hallaka Shao Yunhuan, ’yar jarida dake aiki da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, da Xu Xinghu da matarsa Zhu Ying, wadanda ke aiki da kamfanin jarida na Guangming Daily.

Cikin manyan jami’an da suka halarci bikin na ranar Asabar, har da ministan cikin gida na kasar Serbia Aleksandar Vulin, da ministan kwadagon kasar Darija Kisic Tepavcevic, da babban jami’in ofishin jakadancin Sin dake kasar Tian Yishu.

Game da wannan biki dai, mataimakin magajin garin birnin Belgrade Andreja Mladenovic, ya ce Sinawa da al’ummun Serbia, sun fuskanci muzgunawar kungiyar NATO, wanda hakan ya zamo ginshikin kafuwar kawance mai karfi tsakanin su.   (Saminu)