logo

HAUSA

Ma'aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Bankado Asirin Yanayin Asusun NED

2022-05-09 21:11:47 CMG HAUSA

A kwanakin nan ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wasu jerin shaidu game da asusun demokiradiya na kasar Amurka NED. Kan wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkoki wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau Litinin cewa, wadannan shaidu masu kunshe da manyan sassa shida da kalmomi kimanin 12,000, sun bankado hakikanin tsarin asusun, ta hanyar misalai guda 100 da aka tattara daga rahotanni.

Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, tun da dadewa, kasar Amurka ta yi amfani da karfin tuwo wajen baiwa demokuradiyya makamai, da yaki da demokradiyya da sunan shimfida demokuradiyya, da haddasa rarrabuwar kawuna, da yin katsalandan a harkokin cikin gidan wasu kasashe, lamarin da ya haifar da mummunar illa.

A matsayinsa na mai nuna fin karfi da aikata ashsha da sunan bayar da taimako na gwamnatin Amurka, asusun NED ya keta halascin gwamnatocin wasu kasashe tare da bunkasa makiya masu goyon bayan Amurka ta hanyar fakewa da sunan “inganta tsarin demokuradiyya”.

Zhao Lijian ya ce, asusun demokuradiyya na NED ta kuma fadada aikin makircinta zuwa kasar Sin, tare da zuba kudade masu tarin yawa a duk shekara, don tunzura neman "'yancin kai na Xinjiang, da Hong Kong da Tibet" don aiwatar da ayyukan kin jinin Sinawa. Har ila yau asusun ya yi hadin gwiwa da masu neman ‘yancin Taiwan a wani yunkuri na haifar da rarrabuwar kawuna da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar mashigin tekun Taiwan, lamarin da ya haifar da fushi da adawa daga al'ummomi dake bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan.(Ibrahim)