logo

HAUSA

Kalaman Xi Jinping Game Da Abokantakar Sin Da Koriya Ta Kudu: Makwabtan Dindindin Da Ba Za A Iya Raba Su Ba

2022-05-09 21:25:24 CMG HAUSA

Bisa gayyatar da gwamnatin Koriya ta Kudu ta yi masa, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakin shugaban kasar Wang Qishan, ya jagoranci wata tawaga zuwa Koriya ta Kudu, domin halartar bikin rantsar da shugaba Yoon Seok-youl da za a gudanar a birnin Seoul gobe Talata 10 ga watan Mayu.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi zababben shugaban kasar Yoon Seok-youl a karshen watan Maris, shugaba Xi Jinping ya kwatanta dangantakar dake tsakanin Sin da Koriya ta Kudu da "makwabta na dindindin da ba za a iya shiga tsakanin su ba" da "abokan da ba za su iya rabuwa da juna ba." Ya kuma yi fata sassan biyu za su yi amfani da bikin cika shekaru 30 da kulla huldar diflomasiyya tsakaninsu, wajen girmama, da karfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da kara kyautata hulda tsakanin al’ummominsu, da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Koriya ta Kudu.(Ibrahim)