logo

HAUSA

Firaministan Sin Ya Bukaci A Kara Kokarin Daidaita Yanayin Samar Da Ayyukan Yi Don Cimma Burin Da Aka Sanya Gaba

2022-05-08 18:06:22 CMG HAUSA

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bukaci a kara azama domin taimakawa masu dandalin kasuwanci a kasar wajen daidaita yanayinsu da kuma fadada hanyoyin samar da guraben ayyukan yi.

Li ya yi wannan tsokaci ne, cikin umarnin da ya bayar a taron kasa da aka gudanar ta kafar bidiyo da wayar tarho, game da batun daidaita yanayin samar da ayyukan yi a kasar wanda aka gudanar a birnin Beijing a ranar Asabar 7 ga wata.

Li ya ce, ya kamata a kara kokari don tabbatar da manufar samar da ayyukan yi na wannan shekara wanda aka kudiri aniyar cimmawa.

Li ya kara da cewa, kasar Sin za ta kara azama wajen aiwatar da manufar ba da fifiko ga samar da ayyukan yi, da kuma ci gaba da kiyaye yanayin samar da ayyukan yi da bunkasar tattalin arzikin kasa cikin yanayi mai kyau.

Matakan saukaka wahalhalu kamar rage kudaden haraji da ake karba, za a gaggauta aiwatar da su, musamman ma ga kamfanoni kananan da matsakaita da kuma daidaikun jama’a dake da sana’o’in dogaro da kai, domin rage wahalhalu da kuma kiyaye musu guraben ayyukansu.

Li ya ci gaba da cewa, za a ci gaba da kara himma don bunkasa tattalin arziki, da karfafa gwiwar samar da sana’o’in dogaro da kai masu yawan gaske, da yin kirkire-kirkire, domin samar da karin guraben ayyukan yi.

Firaministan ya kuma jaddada muhimmancin ba da hidimomi, da samar da guraben ayyukan yi ga muhimman rukunonin masu neman ayyukan yi, da suka hada da daliban da suka kammala karatu da ‘yan ci rani, da kuma bayar da gagarumin horo wajen koyar da sana’o’i.(Ahmad)