logo

HAUSA

Hong Kong Za Ta Samu Kyakkyawar Makoma Bisa Sabuwar Surarta Da Sabon Tsarin Zabe

2022-05-08 16:58:35 CMG HAUSA

Ofishin kula da al’amurran yankunan musamman na Hong Kong da Macao na majalisar gudanarwar kasar Sin ya sanar a yau Lahadi cewa, Hong Kong ta koma sabuwa yayin da aka aiwatar da sabon tsarin zabe, lamarin da ke ba da tabbacin samun sabuwar makoma, gami da bude sabon shafi na ci gaban yankin.

Ofishin ya bayyana hakan ne a wani sharhi da aka wallafa bayan lashe zaben da Lee Ka Chiu John ya samu a matsayin kantoman yankin Hong Kong na shida, bayan da ya samu kuri’u da babban rinjaye. Ofishin ya kuma mika sakon taya murna ga Lee Ka Chiu John bisa samun nasara a zaben.

A cewar ofishin, zaben na sabon kantoman yankin, wata babbar nasara ce ga sabon tsarin zaben yankin musamman na Hong Kong tun bayan zaben kwamitin shirya zaben a watan Satumban bara, da kuma zaben kwamitin kula da ayyukan kafa doka na yankin karo na 7 wanda aka gudanar a watan Disamban bara.

Ofishin ya kara da cewa, hakikanin abubuwa sun shaida cewa, sabon tsarin zaben tsari ne mai kyau, wanda yake bin manufar “kasa daya amma tsarin mulki biyu” kuma ya dace da hakikanin yanayin Hong Kong.

Ofishin ya ci gaba da cewa, gaskiya za ta yi halinta cewa sabon zababben kantoman yankin Hong Kong zai ba da jagoranci ga sabuwar gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, da jama’ar dukkan bangarorin al’ummun yankin, da su hada kansu sosai domin samar da kyakkyawar makomar tafiyar da harkoki yadda ya kamata a Hong Kong a bisa sabon mafari. (Ahmad)