logo

HAUSA

Tattalin arzikin Sin ya samu ci gaba mai inganci a rubu’in farkon bana

2022-05-07 16:25:59 CMG Hausa

A cikin kwanakin baya bayan nan da suka gabata, dukkanin larduna da birane 31 na kasar Sin sun fitar da ma’aunin ci gaban tattalin arziki wato GDP a rubu’in farko na bana, inda alkaluma suka nuna cewa, sassa daban daban na kasar sun samu ci gaba mai inganci yadda ya kamata, duk da cewa ana fama da matsin lamba da sauye-sauyen yanayin gida da na kasa da kasa ke haifarwa.

A cikin watanni uku na farkon bana, adadin GDP na larduna 11 dake hade da lardin Guangdong ya zarta kudin Sin yuan triliyan daya, amma a makamancin lokacin bara, lardunan da adadin GDPn su ya zarta triliyan daya 8 ne kacal.

Kana daga saurin ci gaban tattalin arziki kuwa, ban da lardin Jilin, wanda ke fuskantar tasirin yaduwar annobar COVID-19, sauran larduna da birane 30 dake fadin kasar sun samu karuwar tattalin arziki a rubu’in farkon bana, inda wasu lardunan dake tsakiya da yammacin kasar wadanda ke kumshe da Hubei da Shanxi da Xinjiang da Guizhou suka samu ci gaba cikin sauri har saurin ya kai kaso 6 bisa dari bisa makamancin lokacin a bara.

Mataimakin shugaban cibiyar nazarin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare ta kasar Sin Wu Sa, ya yi bayyana cewa, duk da cewa tattalin arzikin yankunan gabashin kasar ba su samu ci gaba cikin sauri ba, suna samun ci gaba mai inganci. (Jamila)