logo

HAUSA

Kwamitin sulhu na MDD ya fitar da sanarwa game da rikicin Rasha da Ukraine a karon farko

2022-05-07 16:19:17 CMG Hausa

Kwamitin sulhu na MDD, ya fitar da wata sanarwa a jiya, wadda ta nuna kulawa ga kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Ukraine.

Sanarwar ta bayyana cewa, daukacin kasashe mambobin MDD suna da hakkin daidaita rikicin kasa da kasa cikin lumana bisa ka’idojin MDD, kuma kwamitin sulhu na majalisar, yana goyon bayan kokarin da babban sakataren majalisar Antonio Guterres yake yi, domin neman samun dabarun daidaita rikicin Rasha da Ukraine.

Kasashen Norway da Mexico ne suka rubuta wannan sanarwa, wadda aka zartas da ita a jiyan. Kana sanarwar ta kasance ta farko da ta shafi rikicin Rasha da Ukraine da kwamitin sulhun ya zartas, tun bayan barkewar rikicin.

Daga baya babban sakataren MDD Antonio Guterres shi ma ya fitar da wata sanarwa, inda ya yi maraba da kudurin kwamitin sulhun na kokarin tabbatar da zaman lafiya a kasar Ukraine.

Ya bayyana cewa, dole ne kasashen duniya su hada kai domin kiyaye ka’idojin MDD, kuma shi ma zai ci gaba da kokari matuka domin ceton karin rayuka tare kuma da cimma burin shimfida zaman lafiya a yankin. (Jamila)