logo

HAUSA

An fitar da alkaluman nazarin kimiyya na na’urar chang’e-5

2022-05-07 16:22:11 CMG Hausa

Rahotannin da aka wallafa a manhajar WeChat na “Babban aikin binciken duniyar wata na kasar Sin” sun nuna cewa, an harhada kyamarar sauka a duniyar wata, da kyamara irin na 360 Panorama, da na’urar binciken ma’adinan gefen duniyar wata, da na’urar binciken samfuran gefen duniyar wata cikin na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-5. A halin yanzu, wa’adin aikin na’urar ya riga ya kai watanni 12, don haka tun daga yau, za a fitar da alkaluman nazarin kimiyya na na’urar bisa “yarjejeniyar sarrafa alkaluman nazarin kimiyya dake shafar duniyar wata da sararin samaniya”, ta yadda za a ciyar da aikin gaba yadda ya kamata. Ana iya karanta alkaluman da abin ya shafa ta hanyar shiga shafin yanar gizo na tsarin fitar da alkaluman duniyar wata da taurari, kamar haka http://moon.bao.ac.cn. (Jamila)