logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu a fashewar Otel na Havana ya karu zuwa 22

2022-05-07 19:30:58 CMG Hausa

Ofishin shugaban kasar Cuba, ya ce adadin wadanda fashewar wani abu ya yi sanadin mutuwarsu a katafaren Otel na Havana dake kasar, ya karu zuwa 22, inda wasu 64 suka jikkata.

Shugaban kasar Cuba Migel Diaz Canel, wanda ya ziyarci wajen da fashewar ta auku da wani asibiti dake yankin, ya ce fashewar ba ta bam ba ce ko hari, hatsari ne.

A cewar ofishin shugaban, ana tsamammnin yoyon iskar gas ne ya haifar da fashewar a Otel na Saratoga.

Ana shirye-shiryen sake bude babban otel din da mazauninsa ke kallon ginin Capitol na tsibirin, a ranar 10 ga wata, a wani bangare na farfado da bangaren yawon bude ido.

Yanzu haka, ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto, yayin da aka karkata hanyoyin mota dake kewayen Otel din. (Fa’iza Mustapha)