logo

HAUSA

Kasar Sin: Yunkurin Amurka na yin tasiri kan kasashen yankin tekun Indiya da Fasifik bai dace da muradun kasashen ba

2022-05-07 19:21:19 CMG Hausa

Dan majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce yunkurin Amurka na samar da karin tasiri kan kasashen yankin tekun Indiya da Fasifik, bai dace da muradun kasashen dake yankin ba.

Wang Yi ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa ta kafar bidiyo da Luhut Binsar Pandjatan, jami’in kasar Indonesia mai kula da dangantakarta da kasar Sin.

A cewar Wang Yi, tuni yankin gabashin Asia ke da tsarinsa na hadin gwiwa karkashin kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato (ASEAN), yana mai cewa kungiyar ita ce jigon tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Ya ce yunkurin Amurka kan yankin ya saba da yanayin na zamani, kuma ba shi ne muradi na bai daya kuma mai dorewa na kasashen yankin ba.  (Fa’iza Mustapha)