logo

HAUSA

Hukumar kula da lafiya ta Sin: Matakan gaggauta shawo kan annoba ba sa nufin kebe wasu ‘yankuna

2022-05-06 19:23:25 CMG Hausa

A yau Juma’a, shugaban tawagar kwararru a hukumar kiwon lafiyar kasar Sin, masu aikin yaki da bazuwar annobar COVID-19 Liang Wannian, ya ce manufar da ake aiwatarwa, ta gaggauta kebe wasu rukunoni domin tabbatar da rage bazuwar annobar, ba ta nufin killace wani babban rukunin al’umma, a kokarin shawo kan cutar baki daya.

Liang ya ce maimakon haka, manufar shawo kan bazuwar cutar na nufin kaucewa killace rukunonin al’ummun kasar, ta dukkanin hanyar da ta dace. Ya ce a halin yanzu, bisa yanayin bazuwar nau’in Omicron na annobar, akwai bukatar karfafa gaggauta daukar matakai, da inganta kandagarki da shawo kan annobar, ta yadda ayyukan sarrafa hajoji za su yi tafiya kafada da kafada da zamantakewar rayuwar jama’a.  (Saminu)