logo

HAUSA

Jimillar kudin shige da ficen hidimomi ya karu da kaso 25.8 a farkon watanni uku na bana a kasar Sin

2022-05-06 13:23:45 CMG Hausa

Rahotanni daga ma’aikatar kula da kasuwanci ta kasar Sin sun ce, daga watan Janairu zuwa Maris din bana, cinikin samar da hidimomi a kasar Sin ya karu cikin sauri. Jimillar kudin shige da ficen hidimomi ta zarce kudin Sin Yuan triliyan 1.45, wadda ta karu da kaso 25.8 bisa dari, inda jimillar kudin hidimomin da aka fitar daga kasar ta kai Yuan biliyan 713.98, wadda ta karu da kaso 30.8 bisa dari, a lokacin da jimillar kudin hidimomin da aka shigo da su kuma ta kai Yuan biliyan 743.01, adadin da ya karu da kaso 21.3 bisa dari.

Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, a farkon watanni ukun bana, yawan hidimomin da aka fitar daga kasar zuwa ketare ya wuce na wadanda aka shigo da su da kaso 9.5 bisa dari, al’amarin da ya haifar da raguwar gibin cinikin hidimomi da kaso 56.4 bisa dari, inda ya kai Yuan biliyan 29.03.

Jami’in ya kara da cewa, cinikin samar da hidimomin ilimi yana karuwa yadda ya kamata, yayin da ake samun farfadowar harkokin shige da ficen hidimomi a fannnin yawon bude ido. (Murtala Zhang)