logo

HAUSA

Shekaru 23 bayan NATO ta jefa bam a ofishin jakadancin Sin dake Yugoslavia, wajibi ne a dauki matakin kaucewa sake aukuwar hakan

2022-05-06 20:58:44 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce a ranar 7 ga watan Mayun shekarar 1999, dakarun kungiyar tsaro ta NATO karkashin jagorancin Amurka, suka jefa bam ofishin jakadancin Sin dake kasar Yugoslavia, wanda ya hallaka Sinawa ‘yan jarida 3, tare da jikkata wasu karin Sinawan dake aiki a ofishin jakadancin sama da su 20.

Zhao ya ce Sinawa ba za su taba mantawa da wannan mummunar ta’asa da kungiyar NATO ta aikata ba, kana ba za su bari tarihi ya sake maimaita kan sa ba.

Zhao Lijian ya kara da cewa, domin tabbatar da tasiri da babakeren ta, da kankane ko ina, Amurka na yin watsi da dokoki, tana aikata duk abun da ta so domin ganin ta dakile kasar Sin a fannonin fasahohin sadarwa.   (Saminu)