logo

HAUSA

WHO: an yi asarar rayuka kusan miliyan 15 sanadiyyar COVID-19

2022-05-06 10:46:56 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, zuwa karshen shekarar 2021, kusan mutane miliyan 15 ne suka mutu a duniya sanadiyyar abubuwan da suke da alaka na kai tsaye, da wadanda ba na kai tsaye ba, da annobar COVID-19.

Bisa kiyasin hukumar, jimilar mace-mace da cutar ta yi sanadi ko kuma karuwar mace-mace fiye da yadda aka saba gani, ta kai kusan miliyan 14.9 tsakanin 1 ga watan Junairun 2020 zuwa 31 ga watan Disamban 2021. An yi lissafin wannan adadi ne bisa bambancin dake akwai tsakanin adadin wadanda suka mutu da wanda ake tsammanin za a samu da cutar ba ta bullo ba, inda aka yi amfani da alkaluman shekarun da suka gabata.

A cewar hukumar, kaso 84 na yawancin karuwar mace-macen ya mayar da hankali ne kan yankunan kudu maso gabashin Asiya da Turai da yankunan America, inda kuma kasashe 10 kacal suka dauki kaso 68 na adadin.

Maza ne suka dauki adadi mai yawa na mace-macen inda suke da kaso 57 yayin da mata suka dauki kaso 43, kana kuma wadanda suka manyata, su ne suka fi yawa cikin alkaluman. (Fa’iza Mustapha)