logo

HAUSA

Kasar Sin ta sanar da daukar karin matakan bunkasa kananan masana’antu

2022-05-06 10:45:57 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Sin ta sanar da sabbin matakan taimakawa kanana da matsakaitan masana’antu, da iyalai masu sana’a, domin shawo kan kalubalen da suke fuskanta.

Yayin da yake jagorantar taron majalisar gudanarwar kasar a jiya, Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya fayyace wasu matakai na karfafa cinikayya da kasashen waje, yayin da ake kokarin inganta tsarin ayyukan masana’antu da na samar da kayayyaki.

Taron ya bayyana kanana da matsakaitan masana’antu a matsayin masu muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi, inda ya ce wasu harkokin kasuwanci na fuskantar karin kalubale, yana mai bayyana bukatar kara tallafa musu.

Baya ga haka, taron ya ce kasar za ta inganta hidimomin da wasu dandali ke samarwa, ciki har da na baje kolin kayayyakin da ake shiga da fitarwa daga kasar Sin, domin karfafa mu’amala da ’yan kasuwar ketare ta hanyar intanet. (Fa’iza Msutapha)