logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Amurka Qin Gang ya yi hira ta musamman da mujallar Forbes kan batutuwan tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka

2022-05-06 18:29:38 CMG Hausa

A ranar 5 ga watan nan na Mayu, shafin intanet na mujallar Forbes ya fitar da labarin wannan hira, wadda a lokacin gudanar ta Jakada Qin Gang ya amsa tambayoyi kan dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, da yarjejeniyar bangarorin biyu kan tattalin arzikin da cinikayya, da zuba jarin na kasuwanci, da yanayin kasuwanci da dai sauransu.

Qin ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka yana fuskantar wasu wahalhalu da kalubaloli, kuma wadannan rashin kwanciyar hankali da rashin tabbas yawancinsu sun fito ne daga Amurka. Don haka ake fatan bangaren Amurka zai daina siyasantar da hadin gwiwar kasuwanci.

Qin ya jaddada cewa, akwai bukatar bangarorin biyu su bi manufar girmamawa juna da kuma fahimta juna, ta yadda za a samu mafitar da bangarorin biyu za su iya karba ta hanyar tattaunawa. Ya ce lokaci ya yi da gwamnatin Amurka za ta sake tunani, tare da gaggauta cire kudaden fito.

Yayin da aka ambato batun zuba jari na Sin a Amurka, Qin Gang ya ce, a shekarun baya bayan nan, banganren Amurka ya dade yana siyasantar da cinikayya da tattalin arziki, ya kuma kakaba takunkumi ga kamfanonin Sin sama da 1000. Don haka muke bukatar bangaren Amurka da ya sauya hankali, kuma ya samar da yanayin zuba jari mai adalci ga masu zuba jari na Sin, ta yadda za su ci gaba da amincewa da kasuwannin Amurka.